Hukumar NEMA Ta Bada Sunayen Jihohin Da Za Iya Fuskantar Ambaliya
Hukumar daukin gaggawa na kasa NEMA Ta Bayyana jadawalin sunayen jihohin 14 da garuruwa 13 zasu iya fuskantar ambaliyar ruwa dalilin ruwan da a iya fuskanta Tsakanin 4 ga watan Yuli zuwa 8 ga watan Yuli.
Bayanin tazo daga jawabi da sa hannun Ibrahim Farinloye kodineta na yanki, daga ofishin yanki na Nema na jihar legas.
Farinloye yana magana dan gwamnati da hukumomi masu daukan mataki, suyi kokari su dau matakan da suka kamata dan tsare rai da dukiyar jama’a.
Ya bayyana jihohi da Garuruwan haka:
Jihar Filato: Langtang, Shendam
Jihar Kano: Sumaila, Tudun Wada
Jihar Sokoto: Shagari, Goronyo, Silame
Jihar Delta: Okwe
Jihar Kaduna: Kachia
Jihar Akwa Ibom: Upenekang
Jihar Adamawa: Mubi, Demsa, Song, Mayo Belwa, Jimeta
Jihar Katsina: Katsina, Jibia, Kaita, Bindawa
Jihar Kebbi: Wara, Yelwa, Gwandu
Jihar Zamfara: Shinkafi, Gumi
Jihar Borno: Briyel
Jihar Jigawa: Gwaram
Jihar Kwara: Jebba
Jihar Niger: Mashegu, Kontagora
Farinloye ya godewa Jan kunne da akayi na ambaliya daga Ministirin Muhalli na kasa na Abuja da bada bayanin.
NAN