ArticlesLabaran Yau

Muhimman Abubuwa 10 Da Makarantu Basa Koyawa Yara

Muhimman Abubuwa 10 Da Makarantu Basa Koyawa Yara

A matsayinka na Uba ko Uwa wanda kuke matukar kaunar ganin cewa ilimin yaranku yatafi da zamani, yazamanto wajibi ku ringa kulawa da abubuwanda ake koyawa yara a makarantunsu. Jami’anmu na Labaranyau sun binciko hanyoyi guda goma wanda yakamata ace ana koyarwa yara a makaranta.

A lokacin da kasar nan bata da halin bawa yara da suka kamala makarantu aikin yi, yana da kyau iyaye su koyar da `ya `yan su wadannan ababe muhimmai wanda zasu taimaka masu wurin rike kansu da kuma samarwa kansu abinyi bayan sun kammala karatu na Firamare, Sakandare har ma bayan kammala Jami`a.

Mother And Children
Mother And Children

Yakamata iyaye su rinka dubawa ta Ina hankalin yaransu ya karkata, Mai suke so Kuma mai suka fi iyawa? Sai a basu karfin gwiwa domin su gane abun da kyau. Idan mutum ko Babba ne ya kasance yana abu ne dan yanaso yafi jindadin yi da Kuma kwarewa.

DOWNLOAD MP3

Wadannan ababe da yara har da manya kansu zasuyi wanda zai basu damar saka Taro da Sisi a aljihunan su domin tsayawa da kafofin su lokacin da gwamnati ta gaza samar da ayyuka a Kasar nan.
Hakika muhimmancin na ababen zaiyi tasiri a rayuwar su idan sun koya aikin hannu zai taimake su a gaba, kuma ya basu ikon daukar wasu aiki ma a lokacin da abubuwan suka zama sun fara biyan su, bayan sun kware a kai a nan gaba, har ma lokacin da suke makaranta kafin su gama, yaro mai hazaka na iya hadawa biyu, yin abubuwan don neman kudi da zai biya wa kansa bukatu kuma ya hada da zuwa makarantar ma duka a lokacin guda.

Abubuwan Guda 10 Sune kamar haka:

1. Yadda ake fara kasuwanci

Koyar da yaranku yadda ake tunanin kasuwanci – yadda ake ganin damar samun kuɗi, yadda ake kashe kudin, da yadda ake nemo kudin shi kansa.

Iyaye na iya ƙarfafa wa yaran su gwiwa ta hanyar koya masu kasuwancin da kuma saka sus u gwada yin kasuwancin a lokacin da suke gaban iyayen na su har sai sun koya kuma an masu gyara a wurin da sukayi kuskure.

DOWNLOAD ZIP

2. Yadda ake yin kasafin kudi

Munanan al’adun mu na kuɗi na al’ada suna tasiri akan yara, shi yasa yawancin mutane ma da girman su ba su san yadda ake sarrafa kuɗi ba.

Koyar da yaranku da wuri. A ba su izinin gudanar da kasafin a gaban iyaye tare da nuna masu kurakurai wurin da sukayi su, zai taimaki yaran sosai a gaba. Misali Iyaye na iya bari yara su ja ragamar tsara kasafin abincin dare a gidajen su tun kafin su girma.

3. Yadda ake rubuce rubuce.

Rubuce rubuce na ɗaya daga cikin mafi kyawun hanyoyin wasa kwakwalwar yara don samun dama da gina hanyar sadarwa.

Rubutu yana daukar salo a wurare kamar irin:

-blog [Kamar wannan kafa ta Labaranyau]
– podcast
– bidiyo
-Twitter

Manufar ita ce nuna wa duniya abin da mutum ze iya yi, kuma ana iya sayar da rubutu. Ƙarfafa yaranku su gina ɗaya.

4. Yadda ake samun galaba a tattaunawa.

Rayuwar nan yanzu cike take da tattaunawa yana da kyau iyaye su koyawa yaransu yadda ake fita daga cikin tattaunawar rashin jituwa, nemo matakin nasara cikin tattaunawa, da bayar da shawarwari na dacewa da ko wanne irin yanayi na rayuwa.

Kwarewar su wurin tattaunawa zatayi tasiri kwarai a rayuwar su nan gaba.

5. Yadda ake yin aiki idan lokacin yi yayi.

Yin aiki na hakika da cimma nasara a cikin aikin muhimmi ne a rayuwa, wannan fasaha ce mai matukar muhimmanci ga mutum.

Koyar da yaranku abubuwan da suka shafi sarrafa ayyuka – da nemo hanya mai sauki domin cimma burin aikin. Kuma mutum ya Sani cewa lokacin aiki da yin aiki bai shafi komai ga yanayin yanda ka tashi ba, ko da fushi ka tashi ko da murna ka tashi ko da rashin jindadi da fushi to mutum yasan dole Sai yayi aiki Kuma ga lokutan aikin.

6. Karfafa wa yara gwiwa wurin yin aikin da suke da shaawar yi.

Da yawa daga cikin mutane an tilasta masu yin ayyukan da basu da shaawar su yi wanda hakan yak an haifar da rashin jajircewa a fannin aikin, a wurin wanna yanayi sai ka ga ba`a cimma ga ci ba. Saboda gajiya da rashin dadin aikin, wani yana da kuzari Kuma yana jin dadin gyara mota wani Kuma yanada karfi amma yafi jin dadin rubutu, kowa da kyautar baiwar da Allah ya masa.

Don haka yana da kyau iyaye su Ƙarfafawa yara don su zaɓi ayyukan da suke da sha’awar suyi, bincikar Muradin nasu, kuma su koyar da abinda suka koya.

7. Yadda ake aiki da kafofin sadarwa

Ilimin sadarwa mai ƙarfi na ɗaya daga cikin mafi kyawun nau’ikan neman kudi.
Yana da kyau iyaye su karfafa yaran su iya mu`amala da mutane ko wanne iri.

– Yaro ya iya bayani da tallata kasuwanci ko sanaar sa , yana da kyau yaro ya iya fasahar zance da kuma bin diddigi.

8. Yadda zasu nuna kansu wurin bukatar hakan.

Sanin yadda ake ƙaddamar da ƙwarewa muhimmin abu ne, iyawa, yadda yaro zai nuna zartar da hukunci lokacin da ya tsinci kansa a inda zai zama dole ya zartas.

Komai tallace-tallace ne. Iyaye su koyawa yaran su yadda zasu sayar da kimarsu da kyau.

9. Yadda ake nemo damarmaki da amfani da su.

Duniya tana cike da damammaki, amma tana zuwa ga waɗanda suka san yadda ake amfani da su.
Iyaye su koyawa yaransu yadda ake nemo damammaki da aiki da su cikin fasaha da tunani na kwarai.

10. Yadda ake kasa gaba

Koyawa yaro yadda zai rungumi darussan rayuwa da kuma yadda zai koyi darasi cikin darasin da ya gani da wanda zai iya riskar sa a rayuwa.

Abubuwa Mafi Muhimmanci Da Yakamata Yan Arewa Su Karkata Akai Sosai

Abubuwa kamar su:

Information Technology wanda ya kunshi Graphic design, Sofware engineering, computer programming, information systems management, computer network, Data science, cyber security, Business Intelligence, Marketing, Data Analytics, Robotics, Artificial Intelligence, web design, Network Security, Cloud Computing, computer engineering da sauransu.

Nasiha

Iyaye karku saka yaran ku dole, ku fahimce su Sai ku karfafa musu. Karku kashe musu burin su sabida baku fahimci abinda suke so ba.

Kar a kashe musu karfin gwiwa, a taimaka musu saboda su taimaka wa kansu da iyaye, yan uwa, abokan arziki da Kuma duniya gaba daya.

Daga: Mawallafa Abdullahi Sudawa da Abdulmatin Dumswak Salihu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button