Labaran Yau

Ziyarar Zaure Zaure Na Hon. Hamisu Cikin Wasu Manyan Anguwanni Dake Kwaryar Bauchi

Hon Hamisu Ya Kai Ziyara Cikin Wasu Manyan Anguwanni da Ke Garin Bauchi

Dan majalissar Bauchi LGA mai jiran gado wanda akafi sani da suna Hon Hamisu Nuru Jibrin ya kai wata gagarumin ziyara wasu manyan anguwanni dake cikin kwaryar garin Bauchi.

Honorable ya samu ganawa da manyan masu anguwanni, masu fada aji dake yankin Tashan Mass, Ganjuwa, Chiroma house da kuma Muhammad Bello Highway Car wash. Kwanaki da suka gabata Hon Hamisu ya samu ziyartan filin kwallon sawu dake federal lowcost cikin garin Bauchi.

Dan takarar majalisan ya ziyarcesu neh don duba lafiyarsu da kuma sanar dasu makasudin fitowansa takara a zaben 2023.

DOWNLOAD MP3

Lallai mutane sun nuna goyon bayansu yayinda suka masa alkwarin bashi duk wata kuri’a don ganin ya kawo chanji a fadin garin Bauchi.

Ga Hotuna ⇓

 

DOWNLOAD ZIP

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button