Tinubu Ya Aika Wa Majalisar Dattawa Sunayen Sababbin Hafsin Sojoji Da Ya Nada Don A Tabbatar Dasu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci majalisar dattawa ta tabbatar da nadin sabbin shugabannin sojoji da ya nada a makon baya.
Bayanin neman tabbatar da su din na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aika wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio kuma aka karanta yayin zaman majalisar na ranar Talata.
Tinubu ya ce bukatar tabbatar da hakan ya yi daidai da dokar kafa rundunar sojin na Najeriya.
A watan da ya gabata ne shugaba Tinubu ya nada Christopher Musa, Manjo Janar a matsayin sabon babban hafsan tsaro (CDS) da Taofeeq Lagbaja, Manjo Janar a matsayin babban hafsan soji.
Ga Hoton Gen Christopher Musa Daga Bisani ⇓
Tinubu ya kuma nada Emmanuel Ogalla, wani babban hafsan sojan ruwa a matsayin hafsan hafsoshin ruwa da Hassan Abubakar mataimakin hafsan sojin sama, yayin da Emmanuel Undiandeye, Manjo Janar aka nada shugaban hukumar leken asiri na tsaro.
Ya bukaci sanatocin na Red Chamber da ta yi duba da bukatarsa cikin gaggawa.
Akpabio, bayan karanta wasikar, ya mika bukatar ga kwamitin na kasa baki daya ba tare da kasancewar kwamitin dindindin na rundunar sojin kasar ba.
Hakan na nufin za a tantance shugabannin sojojin ne a zauren majalisar dattawa, ba a matakin kwamiti ba.