Masu Keke Napep Sun Tuko Daga Lagos Zuwa Abuja Su Girmama Tinubu
Masu tuka keke Napep karkashin kungiyarsu ta Najeriya TOAN sun isa Abuja bayan sun tuko tafiya mai tsayi na kilomita 757 daga Lagos dan nuna girmamawa wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
A hirar da sukayi da jaridar daily trust, Shugaban kungiyar TOAN, ta branch din Ajah, Babatunde Olisah, yace ziyarar sunyi ne dan cikar shugaban kasa kwana 38 a kan karagar mulki da Kuma neman tallafi wa samari da Kuma masu tuka Keke Napep.
Ya ce, “Ni da abokan aiki na biyu, Akintade Temitope da Ahmed Bolaji Mun siyo sabbin Keke Napep dan muyi wannan tafiya.
“Munyi tafiyar mai tsawo na kilomita 757 munyi awa 17 a kan hanya dan mu bada goyon baya wa shugaban kasa da Kuma neman tallafi wa samari da Kuma kungiyar mu.
“Mun kashe naira dubu dari akan man fetur wanda mukayi amfani dashi a tafiyar, Mun tsaya a wurare kamar Ijebu Ode, Akure da Ore kamin muka karaso Abuja dan yabawa shugaban kasa da Kuma neman taimako wa Samarin mu” cewar sa.
Ya bayyana abinda suka fuskanta, Olisa ya kara da cewa yan Najeriya Suna da buri kan sabuwar gwamnati wanda sunga hakan a yayin tahowarsu Abuja daga Lagos, Suna bada shawaran cewa shugaban kasar kar ya watsa wa mutane kasa a ido.