Labaran Yau

BIDIYON DOLLARS: Masana Sun Tabbatar Da Sahihhancin Bidiyon Ganduje Na..

BIDIYON DOLLARS: Masana Sun Tabbatar Da Sahihhancin Bidiyon Ganduje Na

Masana bincike sun tabbatar da sahihancin faifan bidiyo wanda ya nuna tsohon gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje na cika babar rigar sa da bandura na dalar Amurka a shekarun baya yayin da yake gwamnan Kano.

Sanarwar ta fito ne daga bakin Shugaban Hukumar Karbar Korafe korafe da yaki da Cin hanci da Rashawa na Kano Muhyi Rimin Gado a ranar Laraba 1 ga watan Yuli 2023.

A wani taro da Rimin Gado ya shirya na manema labari, ya sanar cewa hukumar ta fara binciken tun shekarar 2018 amma bata cimma nasarar kammalawa ba saboda tsaro da doka ta bawa gwamnan.
A ranar laraba ne hukumar karbar Koeafe korafe da yaki da cin hanci da Rashawa wadda a turance ake kira da Public Complaints and Anti Corruption Commision (PCACC) ta jihar Kano a Rana Laraba 5 ga watan Yuli dinnan ne hukumar ta bayyana cewa faifan bidiyo na Dala ba kerarre bane cewa lallai faifan biyon gaskiya ne.

A shekarar 2017 ne dai aka saki wani faifan bidiyo na tsohon gwamna Ganduje ke karbar Daloli bandur bandur yana zura su cikin babbar rigar sa, dalolin da ake zargin kudade ne na cin hanci da ya tilastawa masu kwangilar ayyuka da gwamnatin jahar kano ta baya ya kasuwa da kamfani kamfani, Vanguard ta wallafa.

A taron manema labarai Muhyi Rimin Gado wanda shine jagoran hukumar ya sanar cewa faifan bidiyo dai ba kerarre bane, Daily Trust ta bayyana.

Wannan sanarwa ta zoh jim kadan bayan hukumar ta damke tsofaffin kwamishinonin na Ganduje guda 5, ciki harda Idris Saleh tsohon kwanishina na Aikace Aikace da Gine Gine na tsohuwar gwamnation Ganduje da ta sauka daga karagar mulkin Kano wata guda da ya wuce. Hukumar na tuhumar tsofaffin kwamishinonin da wadaqa da tsabar kudi har Naira Biliyan Daya N1 Biliyan.

A ranar laraba 3 ga watan Yuli ne dai, Tsohon kwamishinan da wasu biyar sun shiga hannu ne bisa zargin cinye kudi har Naira biliyan daya.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kaddamar da bincike a hukumance kan tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.

Binciken dai na da alaka da faifan bidiyo da ake zargin na karbar cin hanci, wanda ya nuna Ganduje da tarin daloli. Da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata, 4 ga watan Yuli, 2023, a ofishin hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC), Muhuyi Rimingado, shugaban hukumar, ya ce ta na yin katsalandan a binciken.

Sati biyu da suka bata, Mun rawaito cewa, Abba Kabir Yusuf, gwamnan jihar Kano, a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni, ya amince da mayar da Barista Muhyi Magaji Rimin Gado a matsayin shugaban hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa

Da wannan dawowar Rimin Gado zai kammala wa’adinsa na shugaban yaki da cin hanci da rashawa na Kano. Maido da aikin yana tare da sakamako nan take, bisa ga rahotannin kafofin watsa labarai da yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button