Majalisar Dattawan Delta Obedient Elders’ Council ta soki jawabin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wa ‘yan Najeriya a kwanakin baya, inda ta nuna cewa hakan ya nuna rashin alaka da yanayin da kasar ke ciki a halin yanzu.
A wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba, Ciyaman din Chris Biose da Sakatare Solomon Akeni sun mayar da martani kan zanga-zangar da ake yi na #EndBadGovernance a fadin kasar.
Majalisar ta nuna rashin jin dadin ta yadda jawabin shugaban ya kasa magance muhimman batutuwan da suka shafi talakawa.
Sanarwar ta bukaci shugaba Tinubu ya wuce gona da iri da kuma magance matsalolin da ke addabar kasar.
Ta kuma koka da yadda ake tashe-tashen hankula, kwasar ganima, da barnata kayayyakin jama’a da suka haddasa wasu daga cikin zanga-zangar.
Sanarwar ta kara da cewa;
“Shugaban kasar ya amince da tsananin wahalar da talakawa ke fuskanta amma ya kasa gabatar da wasu sabbin tsare-tsare don magance bukatun masu zanga-zangar.”
Majalisar ta bayyana kaduwarta da yadda shugaba Tinubu ya yi watsi da muhimman batutuwa da suka hada da kashe-kashen da Fulani makiyaya ke yi wa manoma, wanda ya yi illa ga samar da abinci a kasar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa,
“Ba shi da ma’ana a yarda cewa bai san cewa wannan al’amari shi ne tushen gazawar manoman Najeriya wajen samar da isasshen abincin da za su ci a cikin gida a cikin ‘yan shekarun da suka gabata.”
Majalisar ta kuma soki gwamnatin kan yadda ta ke ganin rashin bin diddigi da kuma kashe makudan kudade kan wasu abubuwa marasa amfani yayin da akasarin ‘yan Najeriya ke fama da matsananciyar yunwa.
Bugu da kari, sun lura da shirun da shugaban ya yi kan batutuwa kamar satar mai da kuma kisan gilla da jami’an ‘yan sanda ke yi wa ‘yan Najeriya.
Majalisar dattawan Delta ta yi kira da a kara daukar hankali da sanin ya kamata daga shugaban kasa don magance matsalolin da ke addabar kasar.