Yankin Kudu-maso-Gabas ne ke da mafi karancin wakilcin ministoci a cikin wadanda Mista Tinubu ya nada da mutum biyar.
Sanatocin yankin kudu maso gabas sun yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya nada akalla karin ministoci biyu daga yankinsu.
Sanatocin sun ce bukatar tasu ita ce tabbatar da adalci wajen wakilcin dukkanin shiyyoyin siyasa a gwamnatin tasa.
Tony Nwoye (LP Anambra North) ya bayyana matsayin Sanatocin Kudu maso Gabas ta hanyar kudirin da ya gabatar a zauren majalisar a ranar Litinin.
Wasu Sanatoci 14 daga yankin Kudu-maso-Gabas ne suka dauki nauyin wannan kudiri.
Mista Nwoye ya yi korafin cewa yankin Kudu-maso-Gabas ne ke da mafi karancin wakilcin ministoci a cikin wadanda Mista Tinubu ya nada da mutum biyar.
Su ne David Umahi (Ebonyi), Uju Kennedy Ohaneye (Anambra), Nkiru Onyejiocha (Abia), Uche Nnaji (Enugu) da Doris Uzoka (Imo).
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya caccaki Sanatan na Anambra yayin da yake magana kan kudirin.