Labaran YauNEWSPolitics

Ministan Shari’a Abubakar Malami Ya Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takara 2023

Ministan Shari’a Abubakar Malami Ya Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takara 2023

Ministan shari’a kuma Antoni Janar na ƙasar nan, Abubakar Malami, ya bayyana shirinsa na neman takarar gwamnan Kebbi a babban zaɓen 2023 dake tafe.

This Day ta rahoto cewa Malami, wanda ya bayyana shirinsa a gaban dandazon masoyansa, ya ɗauki alƙawarin ba zai ci amanarsu ba.

Malami, SAN, ya bayyana cewa shugabanni na bukatar magoya baya, haka nan magoya baya na bukatar shugabanni su tabbatar mutane sun amfana da jagorancin su.

Bugu da kari, ya lashi takobin yin aiki ba dare ba rana dominn tabbatar da ya canza rayuwar al’ummar jihar Kebbi.

A baya dai, wasu rahotanni sun nuna cewa Malami ya shaida wa abokansa na kusa cewa yana kwaɗayin shiga zaɓen jihar Kebbi.

Babu tantama zai nemi takara ne a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC kuma zai nemi ya ɗora daga inda gwamna Atiku Bagudu ya tsaya, wanda zai kammala zango na biyu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button