Labaran Yau

Yan Sanda Sunyi Nasaran Damke Jami’in Tsaron Rarara Wanda Yayi Harbi..

Yan Sanda sun kama jami’in tsoron da keh tsare Rarara dan yayi harbi a sama

Hukumar yan sanda ta kasa ta shaida an kama yan sandan da suke jikin mawakin siyasa ta APC, Dauda Kahutu Rarara, Akan harbi da sukayi da kananan bindiga dan murna wanda ya fita ka’ida.

A bidiyon da ta bazu a shafin sada zumunta, yan sanda guda biyu da keh jikin shi an gansu suna harbi sama, shi Kuma an gano shi yana tafiya zuwa motarsa a inda ayi pakin dinta bayan ya gama Rabon kayan matsarufi wa mutane dan watan Ramadan a kauyansu kahutu a jihar katsina.

Akan lamarin harbin da yan sandan sukayi, Meh magana da yawun babban ofishin yan sandan Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana a shafinsa na Twitter, cewa an gano yan sandan guda biyu Kuma zasu bayyana a babban ofishi dan ansa tambayoyi wajen masu horo a Abuja.

DOWNLOAD MP3

A bayanin, “Hukumar yan sanda ta kasa ta nuna hakan ba kwarewa bane da rashin tarbiya ta yan sanda na harbin bindiga dan nuna isa na mawakin a kano kwana kin baya.

“An gano yan sandan kuma an kamasu suna tsare, Kuma za a kaisu babban ofishi dan ansa tambaya da ladabtarwa dan hakan bata cikin tsarin yan sanda Kuma hukumar barata Lamunta ba.

“ Kuma Muna yabawa masu kishin kasa da suka tura mana bidiyon dan daukan matakin da ya dace, Zamu cigaba da kawo sabbin hanyoyi dan inganta aikin yan sanda”

DOWNLOAD ZIP

Daily nigeria ta rawaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button