AddiniLabaran Yau

Aqeedar Sunnah Ko Bidi’ah Wacce Ce Gaskiya

Aqeedar Sunnah Ko Bidi’ah Wacce Ce Gaskiya

Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Rahimahullah, Yace “Magana ce guda biyu ko kayi sunnah ko kayi bidi’ah, babu wani kwane kwane. Wai ni abinda nake jin haushi idan aka ce darika, Ta Tijjani ace Tijjaniya, Qadiriyya ta AbdulQadiri, Shazaliyya ta Shazali, Rufa’iyya ta Ahmadu Rufai, wacece ta wane.

“Amma ita sunnah, Ita sunnar ta wa? Ta Ibn Taimiyya? Ta Mahmud bn AbdulWahab? Ta Marigayi Sheikh Mahmud Abubakar Gumi? Sunnar Wa? Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam.

“Sai ka fada mana inda zaka, in aka ce Ahlussunnah, Sai kace ni ba Ahlussunah bane Wai dan jin tsoron kar yan darika suyi fushi dashi, ya waare kenan. billahilladhi mun ware Mun Kuma waarewa mu Ahlussunnah ne in shaa Allahu”

Sheikh Abdulrazak Haifan
Sheikh Abdulrazak Haifan

Ba’a Bada Aure Ga Masu Bidi’ah

A littafin Al Mudawwana na Imamu Maalik, Sheikh Abdulrazak Haifan Ya gabatar, “ Ba a bada aure ga masu Bidi’ah, ba a karban aurensu Kuma ba a basu aure, ba a musu sallama, ba a sallah a bayansu.

“In sun mutu ba a halartan jana’izar su cewar Imamu Maalik, Al Mudawwana Littafi na Fiqhu ne sananniya. Kuma Imamu Ahmad Bn Hanbal shima ya fadi haka. Maganar AlFudair Bn Iyab da yake cewa idan mutum ya dauki yar sa ya bada aurenta wa mai Bidi’ah, ya yanke zumuncin ta. Wannan Gaskiya ne, Sai yace duk wanda yabi jana’izar yan bidi’ah, bazai gushe ba yana cikin fushin Allah har Sai ya dawo gida.

“Wannan yana daga cikin tsanantawa da Ibn Iyab ya keyi saboda tsoratar damu hadarin Bidi’ah ga musulmi. Amma asalin hukuncin Al Imamu Maalik, Imamu Ahmad Bn Hanbal basu halarta jana’izar mutumin da yayi Bidi’ah kuma sannan basu cewa kar aje, basu hanawa idan akayi rasuwar mutumin da yana Bidi’ah zasu bari aje jana’izar sa, koh da a gidan ne, yayansu zasu je barasu hanasu ba.

“Amma su basuyi, abinda yasa saboda ya zama abun misali ga masoyan su, su gane hadarin Bidi’ah”.

Dan karanta fatawa daga Bakin Malamai

Gar zayo shafin labaran.com.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button