Labaran Yau

Gwamnatin Buhari Ta Kirkiro Ayyuka Miliyan 12 Cewar Fadar Shugaban Kasa

Gwamnatin Buhari ta kirkiro ayyuka Miliyan 12 Cewar fadar Shugaban kasa

Garba shehu, babban mai taimaka wa Shugaban kasa kan zantar da sakonni. Yace mulkin shugaba Muhammadu buhari ta kirkiro ayyukan yi wa mutane miliyan sha biyu a fannin noma.

Shehu, a tattauna war sa da tashan channel TV wanda akayi karkashin Sunrise Daily, yace mulkin tayi kokari a fanni daban daban wanda sun hada da tsaro, wutan latarki, yaki da cin rashawa da sauransu.

“A noma kawai, kungiyar masu noman shinkafa tana maganan ayyuka miliyan goma sha biyu, kuka abinda mukayi, wannan gwamnatin ta gaji kampanin taki hudu amma yanzu muna da kampanin taki hamsin da biyu wanda ke aiki yau.

DOWNLOAD ZIP/MP3

“An maida bada taki wa masu noman shinkafa Miliyan goma sha biyu, yanzu masu noman shinkafa Suna sarrafa shinkafa a gida. Wanda yasa kasan ta samu isheshshen abinci. Mun kawo wasu hanyoyin samu arziki wa kasa, hanyar samun kudi wa kasa ba guda bane yanzu kamar yadda muka sameta.

“Kasar ta kashe dala biliyan biyar a kullum wajen siyo shinkafa kamin mu shigo mulki, yau babu dala daya da ke fita dan sayo shinkafa a waje” a cewar sa.

Akan rashawa, shehu yace Shugaban baida wata asusu a banki wanda akayi ajiya na kudin rashawa Kuma bayi tsoron tuguma bayan yabar karaga.

“A matsayina na mai magana da yawun Shugaban kasa, Ina kwanciya inyi barci lafiya babu kokwanton za a kirani kan cewa an ga wata asusun kudade wanda Shugabana ya boye, a Najeriya ko kasar waje, wannan ba Buhari bane, yafi karfin hakan” in ji shi.

Daily trust ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button