Labaran Yau

Jam’iyyar Adawa Sun Janye Neman Shugabancin Majalisan Tarayya

Jam’iyyar Adawa sun janye neman Shugabancin Majalisan tarayya

Zababbun yan Majalisun tarayya na jam’iyyar adawa, sun janye neman Shugabancin Majalisan tarayya na 10 kamin kaddamar da Majalissa ran biyar ga watan yuni.

Jam’iyyar adawa sun janye neman kujeru biyu na Shugaban da mataimaki na Majalisan tarayya saboda basu da kudirin takarar.

Afam Vogene, Mai magana da yawun jam’iyyar adawa ya bayyana hakan a zaman da sukayi a Abuja.

Yace babu dan majalisa a cikin su na yan kadan cikin Majalisan da ya nuna kudirin neman takarar.

Jam’iyun adawan sun hada da PDP, LP, NNPP, AFD. Wasu daga ciki sun hada da YPP, APGA da SDP.

Ita hadakaiyar wanda ake kira da “great majority” ta kashe kudirin ta na takarar shugabancin Majalisan dan kwace karagar mulki.

Kwamitin mutum goma sha daya aka nada dan duba tantance wanda yakamata suyi takarar.

Mista Ogene bayan aiwatar da aikin kwamitin, babu wani dan majalisa da yayi wani hubbasa dan ya nuna niyya ko da na Burga dan takarar ba.

Ogene ya kara da cewa sun bi wasu yan Majalisu na APC wanda wasu suka cancanta. Sauran bayanin yace sai sun gama tattauna wa kamin a bayyana.

Duk da hakan ita kungiyar za ta zauna mazaunin tsintsiya guda a matsayin su jam’iyun adawa.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button