Sakacin Suwaye Harin Da Akakai Kan Jirgin Qasa- Falana
Babban lauyan nigeria Femi falana (SAN) ya Allah wadai tare alakanta harin da aka kai kn jirgin qasa mai tashi daga Kaduna zuwa kaduna ga ministan sufuri Rt Hon Rotimi Amaechi da Babban Manajan hukumar kula da harkokin jiragen qasan Najeria Mr Fidet Okhiriat.
Mr Femi Falana Yayi Da a gurfana dasu a gaban Kotu A takardan da wallafa yau Litinin.
Yace rashin sanya ido da ko in kula da ministan sukayi da hukumar shine ummul aba’isan aukuwan Harin. sam babu wani matakan tsaro da suka shirya don kula da hukumar- cewar Mr Falana.
Dukda sunsan hanyar Kaduna zuwa Abuja Sam Babu isheshshen tsaro, amma a haka suka bar mutane da rahotannin karya. Tunda Hakane dole bazaa sanya idanu tare da barin rayukan yan nijeriya a hannunsu ba, Kuma yazama wazibi a gurfanar dasu.
Yazama wajibi Hukumar ta dauki nauyin jinyan duk wanda yaji rauni sanadiyyar harin tareda biyansu diyya Musamman mutanen da masu garkuwa da mutane sukayi awungaba dasu.