Labaran Yau

Maiyaki Ya Samu Rikon Kwaryar Shugabancin NUC

Maiyaki Ya Samu Rikon Kwaryar Shugabancin hukumar Jami'a Ta Kasa NUC

Mataimakin Executive sakatare na hukumar jami’a  ta kasa NUC, Mista Chris Maiyaki ya cigaba da kula da gudanar wa na Hukumar kamin a zabi Shugaban.

Mai Murabus kan shugancin NUC Farfesa Abubakar Rasheed ya mika karagar mulki wa Maiyaki ranar jumma’a a wani karamin taro da akayi da tsohon shugaban Hukumar Farfesa Julius Okojie, mambobin daraktoci na Hukumar da manyan baki wanda ya hada da tsoffin VC’s na jami’o’i.

Farfesa Rasheed zai koma jami’ar Bayero a Kano, inda zai koma bakin aikinsa na koyarwa ran daya daga watan yuli shekarar 2023.

An bawa maiyaki mukamin mataimakin shugaban Hukumar ta NUC a shekarar 2020.

Kamin nan, shine darakta na ofishin shugaban DESO, lokacin da Farfesa Rasheed ya kawo shi NUC a shekarar 2017 inda yayi aiki a ofishin sa a na mataimakin shugaban a Hukumar.

Maiyaki ya karanta International Relations a jami’ar Ahmadu Bello na Zaria, ya kara karatun digiri na biyu a fannin international Law and diplomacy a jami’ar Jos. Ya Samu horaswa a gida da wajen Najeriya wanda ya hada international Affairs da Educational planing, Accreditation da quality Assurance,  Parnership da collaboration, procurement da project management, computer application in human resource management, higher education management, regulation da knowledge diplomacy da sauransu.

Ya fara aikin gwamnati shekaru talatin da suka gabata a matsayin administrative officer I, a shekarar 1990 a Policy and administrative arm na ofishin gwamna a Jos jihar filato.

Ya koma offishin Hukumar jami’an NUC inda ya samu canjin aiki a shekarar 1993, bayan nan aka bashi matsayin sakatare na aikin bankin duniya world bank wanda akeyi a NUC, yayin da yayi aikin jami’a ashirin na kimanin dala miliyan dari da Ashirin.

Bayan kammala aikin bankin duniya, wanda ya kasance mafi inganci a harkar ilimi na Najeriya, a shekarar 1996 ya yayi aiki a wurare daban daban a Hukumar har dai da yakai mataimakin darakta na special duties da shugaban Ma’aikatan ofishin Executive sakatare na Hukumar, daga nowamba 2009 zuwa oktoba 2014 inda ya zama darakta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button