Labaran Yau

Nijar Ta Karyata Maganar Kona Ofishin Jakadancin Najeriya Da Ke Nijar

Ofishin Jakadancin Najeriya a Jamhuriyar Nijar ya musanta rahotannin da ke cewa an kona gininsa, Ofishin jakadancin Najeriya a jamhuriyar Nijar ya musanta rahotannin da ke cewa an kona gininsa.

A cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin ya fitar, ya ce masu zanga-zangar sun yi yunkurin shiga ginin Chancery da ke Naimey, babban birnin Nijar a ranar 30 ga watan Yuli, amma sojojin Nijar da na ‘yan sanda sun hana su shiga.

Ofishin jakadancin ya kara da cewa a halin yanzu ginin nasa yana da kariya daga sojojin Nijar da sauran hukumomin tsaro.

Ga sanarwar da ofishin jakadancin suka bayar a kasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button