Labaran Yau

Bidiyon Rarara Tareda Mahaifiyarsa Bayan Yan Garkuwa Sun Sakota

’Yan garkuwa da mutane sun sako mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa dake jamiyar APC, Dauda Abdullahi Kahutu Rarara, da suka yi garkuwa da ita makwanni daya gabata.’

Masha Allah bayan shafe tsawon mako ana cikiyar maman mawakin APC wato Dauda Kahutu Rarara yau laraba masu garkuwan suka sakota.

Dauda Kahuta Rarara Da Mahaifiyarsa
Dauda Kahuta Rarara Da Mahaifiyarsa

Alhamdulillah cikin hukuncin Allah yau mawaqi Rarara ya samu damar ganawa da mahaifiyarsa bayan ansha gwagwarmaya tsakaninsu da yan bindiga.

Ga abinda Aisha Humairah ta fada a shafinta

“Ina Mai Matukar Godiya Ga Ubangiji Na
Ina Godiya Yan Uwa Da Abokan Sa’a Ta
Ina Godiya Masoyana Na Fadin Duniya Baki Daya

Hakika Banida Bakin Godiya A Gare Ku”

Ga Bidiyon Rarara Tareda Mahaifiyarsa Dan Kasa Kadan ⇓

Yadda Yan Bindiga Suka Sace Mahaifiyar Dauda Kahutu Rarara

Ranar 28 ga watan Yuni, akayi garkuwa da Hajiya Halima wanda akafi sani da mahaifiyar Dauda Kahutu Rarara.

Yan bindigan sun dauketa ne a gidanta da ke yankin Kahutu a wanda ke Karamar Hukumar Danja ta Jihar Katsina.

Shaidu daga kauyen sun yi bayani kan cewa an sace maman Rarara ne da misalin karfe daya na dare wasu dandazon ’yan bindiga suka kutsa gidan dattijuwar suka yi awon gaba da ita.

“A kafa suka zo, ba su yi harbi ba a lokacin da suka kai harin suka yi garkuwa da ita cikin ’yan mintoci.

“Dattijuwar ba ta bijire musu ba  a lokacin da suka nemi izinin ta biyo su.

“Duk da cewa ’yan bindigar sun samu wasu mutane a gidan, amma mahaifiyar Rarara kadai suka dauka.

“Babu wani yunkuri da aka yi na tunkarar ’yan bindigar a lokacin da suke tafiya da ita saboda bindigogin da suke dauke da su,” in ji wani mutum mazaunin kauyen Kahutu.

Yakara da cewa;

“Watakila maharan sun bar baburansu ne daga nesa suka tako zuwa cikin kauyen a kafa.

“Muna rokon Allah Ya kubutar da ita cikin koshin lafiya domin tana taimaka mana sosai a wannan kauyen.

“Danta Rarara mai yawan taimakon al’umma ne, kuma ya kawo mana abubuwan cigaba sosai a garinmu,”

Cewar mazaunin Kauyen Kahutu.

A matsayinmu na gidan jarida meh kishin kasa Labaranyau taya Rarara murnan ganin mahairfiyarsa kuma muna fatan Allah yakare nagaba kuma ya kare mana kasarmu Najeriya baki daya.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button