Labaran YauNEWS

2023-Zan Nuna Bajintata Idan Na Zama Shugaban Kasar Nigeria

2023-Zan Nuna Bajintata Idan Na Zama Shugaban Kasar Nigeria

Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya bayyana cewa zai nuna bajintarsa wajen gudanar da shugabancin Nijeriya, acewarsa yana son mulkin ne don kishin Nijeriya da ‘yan kasar.

Dubban yan Nijeriya ne suka yi dirar mikiya a dandalin Eagle Square da ke Abuja, babban birnin kasar, yayin da Gwamna Yahaya Bello yake ayyana wa a hukumance aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a 2023.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Wurin da aka gudanar da taron ya cika makil, an ga jama’a ciki da wajen filin taron, tare da kungiyoyin tallafi da dama sanye da tufafin Yahaya Bello nau’i daban-daban suna rera wakokin siyasa.

Saidai akasarin wanda suka taru wajen kaddamar da aniyar Gomna yahaya bellon  yen wasan kwaikwayo ne na kanywood.

A ‘yan watannin baya-bayan nan dai an sha jin kiraye-kirayen kungiyoyin matasa da mata daban-daban a fadin Nijeriya na neman gwamnan jihar Kogi ya tsaya takarar shugabancin tarayyar Nijeriya.

Gwamna Bello ya kaddamar da Sanata Jonathan Zwingina da diyar marigayi MKO Abiola, Hafsat Abiola a matsayin kodineta na kasa da darakta janar na yakin neman zaben sa da aka fi sani da ‘Hope 2023: Yahaya Bello Presidential Campaign Organisation’.

Da yake bayyana aniyarsa ta tsayawa takara, Gwamna Bello ya ce ya nuna bajinta sosai akan shugabancinsa a jihar Kogi, don haka zai iya jagorantar Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button