Gwamnatin jihar Ondo ta fara biyan naira biliyan 3.2 a matsayin kyauta ga ‘yan fansho a jihar.
Biyan wanda ya hada da kyauta da ake bin wadanda suka yi ritaya daga shekarar 2015 a karkashin tsarin fansho na jihar, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ne ya bayyana hakan yayin wani biki a Akure.
Gwamnan ya bayyana cewa za’a ware naira biliyan daya ne domin biyan ‘yan fansho da suka yi ritaya daga kananan hukumomi a shekarar 2012 da 2013, yayin da naira biliyan 2.2 za a ware tallafin na 2015 ga ‘yan fansho na jiha.
Aiyedatiwa ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da samar da ababen more rayuwa ga al’ummar jihar, ya kuma yi alkawarin kara daukar matakan shawo kan matsalar basussukan da ake bin su a wasu shekaru masu zuwa.
Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Mista Amidu Takuro, da shugaban kungiyar ’yan fansho ta Najeriya a jihar, Mista Johnson Osunyemi, sun yaba wa gwamnan bisa yadda ya yi jawabi na kyauta.
Wadanda suka ci gajiyar tallafin da suka hada da Mista Adedayo Ajayi, suma sun nuna jin dadinsu da biyan.