Labaran Yau

Yan Sanda Sun Kama Masu Diban Ganima 57 A Garin Kano

Yan sanda sun kama masu diban ganima 57 a garin kano

Ofishin yan sandan jihar kano, ranan Jumma’a ta kama Ta kama mutum 57 kan zargin satar kaya a jihar.

Jawabin tazo cikin bayanin da dan sanda mai magana da yawun ofishin SP Abdullahi Haruna Kiyawa a garin Kano.

Haruna Kiyawa ya bayyana cewa kwamishinan yan sanda, Mohammed Usaini Gumel yace kamen da akayi ya faru ne kan tsarin dokar kare rayuka da dukiyan Al’umma a jihar.

Usaini Gumel ya dauki matakin lura da sumame bayan rahoton cewa yan tada zaune tsaye suna cin moriyar rushe rushen da akeyi na gine ginen baya kan doka da gwamnati keyi wajen satar dukiyar mutane.

Hukumar labarai ta kasa, ta bada rahoton cewa ofishin yan sandan ta kama mutum 49 ran 5 ga watan yuni, wanda an dukufar dasu gaban kotu.

Kwamishinan yan sandan yace dukiyar aka iya dawo dasu sun hada da kofofi, tagogi, Bulok da rodi acikin wanda aka sata.

“An bada shawaran kai masu dukiyar da aka satan musu dasu je ofishin tsaro da binciken laifuka na jiha ta Kano Bompai, dan ansa kai karar su ko ta wannan lambar 08038249455” a cewar sa.

Gumel ya yabawa wanda suka bada bayanai da yakai da kama wanda suke da hannu kan laifin da Kuma dawo da wasu kayayyaki.

Ya bada shawara wa shugabanni da iyaye da su ja wa yaransu kunne su daina satar kayan mutane da sunan ganima, saboda Duk wanda aka kama zai fuskanci doka.

“In samu matsala za a iya tuntubar yan sandan jihar kano a wannan lambar, 08032419754, 08123821575, 09029292929” cewar dan sandan.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button