Labaran Yau

Ni Uban Gidan Ganduje Ne Cewar Kwankwaso

Ni Uban Gidan Ganduje ne cewar kwankwaso

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Kayan marmari NNPP, a zaben da ta gabata a shekarar 2023, Kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu kwankwaso ya bayyana tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje dan sa ne a siyasa dan bare iya kallon sa a ido ba.

Kwankwaso ya mai da martani bayan ganduje yayi alwashin marin sa in sun hadu a fadar shugaban kasa na Villa ran jumma’a.

Sanata kwankwaso da Ganduje sun halarci Villa ranar jumma’a, yayin da kowannan su ya bayyana cigaban jiha wa Shugaban kasa Bola Tinubu.

Hirar da BBC hausa tayi da Kwankwaso ranan Asabar. Mista kwankwaso yace tsohon gwamnan yana rude yayin da ya furta wannan kalamai.

Naji ance shi (Ganduje) yace zai mare ni, amma shiririta ne. Ya rude ne kuma shi yarona ne a siyasance. Barasu iya kallona a ido ba in Mun hadu. Yana cikin rudani ya fadi hakan. Idan suka ganni saukar da kai sukeyi” a cewar sa.

Tsohon dan takarar shugaban kasan yace shugaban kasa ya razana bayan ya bayyana mishi abubuwan da ya aikata.

“Wasu sunje sun mai karya (Tinubu), bayan na bayyana mai Gaskiya, Yayi mamaki kan cewa gwamna ya siyar da Department na jami’a, ya rusa, wanda ya gina shaguna wa kansa”.

Ya Kuma yi zargin shi tsohon gwamnan da siyar da filaye na filin wasanni, fillin Alhazai (Hajj Camp) da Kuma fillin idi wa iyalensa da mutanen sa.

Yayi magana kan zargin da akeyi cewar gwamnatin jiha bata bada sanarwa ba kamin rushe rushe ba, cewar sa sabon gwamna yana aikine bisa alkawarin da yayi kamin zama gwamna.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button