Labaran Yau

Ko Kasan MTN Da Airtel Sun Fi Kowane Kudi A Nigeria? Ga Cikakken Bayani

Ko Kasan MTN Da Airtel Sun Fi Kowane Kudi A Nigeria?

Kamfanin MTN Nigeria da Airtel Nigeria sun zama kanfanonin da suka fi samun jari a kasar nan da Naira Tiriliyan 5.56 da Naira Tiriliyan 4.49, yayin da sauran kamfanonuwa guda 8 ke biye da su a baya akan manyan kamfanoni 10 na musayar hannun jari a cikin watan Yuni.

A cikin wata sanarwa da musayar ta fitar a jiya, kamfanonin sadarwa biyu na hada-hadar jarin N10.5tr ya bai wa bangaren ICT kwarin gwiwa kan bangaren kayayyakin masana’antu da ke jerin Dangote da BUA da jarin N7.98trn, da kuma bangaren kayayyakin masarufi. wanda ke da Nestle da BUA da N3.43trn.

Bayanai sun nuna cewa bangaren hada-hadar kudi ya samu N2.11trn yayin da mai da iskar gas ke da N823.7bn da kuma bangaren kayan aiki N750bn.

A cikin shekaru ukun da suka gabata, bangaren ICT ya jagoranci sauran bangarori wajen bayar da gudummawar da suke bayarwa ga GDP na kasar nan.

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce masana’antar sadarwa ta samu jarin sama da dala biliyan 70 a cikin shekaru 22 da suka gabata.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button