Jagorancin ECOWAS Da Aka Bani Abun Mamaki Ne Gareni
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da juyin mulki da ke faruwa a yankin yammacin Afirka. Tinubu a matsayin s ana sabon shugaban kungiyar shugabannin kasashen yammacin Afirka a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli.
Shugaban Najeriya ya yi Magana da sauran shugannin da su rungumi dimokradiyya sannan kuma yayi alkawarin inganta tsarin mulkin dimokradiyya a fadin yammacin na Afrika da zai fara jagoranta.
A kasar ta Bissau, Guinea-Bissau – Sabon shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu, ya ce matakin da sauran shugabannin kasashen Afirka suka dauka na nada shi baki daya a matsayin shugabansu, abin mamaki ne.
Tashar talabijin ta Arise ta bayar da rahoton cewa, yayin da yake jawabi a taron shugabannin gwamnatoci karo na 63 a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli a birnin Bissau na kasar Guinea-Bissau, shugaban na Najeriya ya kuma sha alwashin cewa kasashen yammacin Afirka za su yi kakkausar suka ga juyin mulki.
Shugaba Tinubu, wanda shi ne na baya-bayan nan da ya shiga kungiyar ta musamman ta shugabannin kasashen yammacin Afirka, ya karbi wannan karramawa cikin farin ciki, tare da yin alkawarin daukar nauyin ofishin da tafiyar da harkokin gudanarwar kungiyar ta yankin, a cikin jawabin nasa.
A game da matsalar juyin mulki a yankin, Tinubu ya ce: “Ba za mu bari a yi juyin mulki bayan juyin mulki a yankin yammacin Afirka ba. “Za mu dauki wannan da mahimmanci, tare da Tarayyar Afirka (AU), kuma za mu mika takarda zuwa Tarayyar Turai (EU), da Burtaniya, da Amurka domin samun goyon bayan su.
Ni na Dauke shi kalubale mai girma.
Dimokuradiyya tana da matukar wahala a gudanar da ita, amma ita ce mafi kyawun tsarin gwamnati, kuma dukkanmu muna bin ta.
“Ya kamata mu yi alkawari a nan cewa, a ci gaban tattalin arzikin yankinmu da bunkasuwarmu, za mu himmatu wajen tabbatar da dimokuradiyya, da inganta dimokuradiyya, da bin doka da oda.
A Najeriya mun dawo.” Ya ci gaba da cewa: “Dole ne mu koma baya. Ba za mu iya zama kamar karnuka marasa hakori a ECOWAS ba. “Saboda amincewar da aka yi mini, na yi muku alƙawarin , cewa zan yi iya ƙoƙarina.
Ni sabo ne kawai. Wannan shi ne na farko; An ba ni fakitin ban mamaki, Za mu yi aiki tare don ci gaba da haɗin gwiwar tattalin arzikin yankin Afirka ta Yamma. “kuma zamu dauki matakin hana cin zarafin mutanen yankin namu na Afrika ta yamma da wadansu sauran mutanen da ba mu ba sukeyi.”