Advertisements
Roma Zasu Dauki Romelu Lukaku A Matsayin Loan
Chelsea sun amince da tafiyar Lukaku zuwa Roma a matsayin loan. Lukaku ya buga loan a Inter Milan a season daya gabata. Yazo Chelsea ne akan kudi £97.5m daga Inter Milan a watan August 2021.
Officials na Roma sun tafi London a karshen satin daya wuce domin yin magana fiska da fiska akan zuwan Lukaku Roma, Chelsea da Roma sun yarda da tafiyar Lukaku loan a kan kudi da bai wuce £8m ba.
Lukaku ya nuna farin cikin sa na tafiya League din Italy a Roma, saboda son buga wasa a karkashin tsohon kocin sa Jose Mourinho. Juventus sun fara magana da Chelsea akan sayan Lukaku a watan baya na farkon season.
Advertisements
Kungiyar kwallon kafa Al-Hilal na Saudi Arabia ma sun nuna sha’awar sayan Romelu Lukaku dan shekara 30 daya zo Chelsea daga Inter Milan a kan kudi £97.5m.
Advertisements