Tottenham Sun Ci Mutuncin Manchester United Da Kwallo Biyu da Babu
Tottenham sun saka kwallo biyu a ragan Manchester united a gasar premier league ta jiya wato 19 ga watan Ogusta.
Hakan ya faru ne bayan minti hudu da dawowa daga hutun rabin lokaci, wanda “Dejan kulusevski” ya yanko ketararriyar kwallo wadda ta taba Martinez, kafin ta tafi a dai-dai wajen “Pape sarr” dan shekara 20, ya shigar da ita ragar Manchester united.
Pape sarr yaci kwallon sa na farko a Tottenham, wanda shi ne yasa Tottenham a matakin nasara bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
VAR ya kashe bugun ‘kai tsaye da gola’ (penalty) wadda Manchester united suka nemi a basu a minti 28 na farkon rabin lokaci.
A cikin minti 36 na farko, Man united ta kai hari masu yawa zuwa ragar Tottenham amma bata samu nasarar shigarda kwallo ko daya ba.
Tottenham sun tabbatar da nasara ne lokacin da “Lisandro Martinez” yaci gida a yunkurin cire kwallon da “Ben Davies” ya kawo hari ana saura minti 7 a hura tashi.
Aaron wan-bissaka ya samun yellon kati a dalilin nuna fusatansa, bayan alkalin wasa ya hura mummunan shiga dayayi wa Heung-min Son a farkon rabin lokaci,
Anthony yayi mummuna shiga wa Yves Bissouma a farkon rabin lokaci, hakan ya jawo alkalin wasa ya bashi yellon kati, sannan ya hada da kaftin Bruno Fernandez saboda korafin dayayi.
Bayan wasu mintuna da dawowa daga hutun rabin lokaci, Alkalin wasan ya sake bawa “Iyenoma Udogie” yellon kati saboda bata lokacin dayayi bayan tsayarda wasa.
Sabon golan Tottenham Guglielmo vicario yayi nasarar hana kwallo shiga ragar sa. Ya nuna jarumta a wasan sa na farko a Tottenham, bayan hana kwallaye dayawa shiga raga, tareda ture kwallon “Marcus Rashford” wadda sukayi gaba-da-gaba.
Tottenham sun tafi da maki uku, tareda saka mabiya bayan Tottenham farin ciki.
Wannan wasan ya zama kaman gargadi ga Erik Ten Hag Kocin Manchester united domin sake duba matsalan dake tareda tsarin yan wasanni a kungiyar.
Ange Postecoglou Sabon kocin Tottenham yayi nasara a wasan sa na farko a gida wajen cin babban kungiyar kwallon kafa na Ingila wato Manchester united.