
Chelsea Ta Kammala Yarjejeniyar Sayan Dan Wasan Tsakiya Na Kasar Belgium Daga Southampton
Kungiyar Chelsea ta kammala sayan dan wasan kwallon tsakiya na kasar Belgium wato Romeo Lavia daga kungiyar kwallo ta Southampton akan kudi £58M, ya sa hanu a kwantiraki na tsawon shekaru 7 a Chelsea ranan Juma’a 18 ga watan Augusta.

Liverpool tayi sha’awar dan wasan Romeo lavia, amma Southampton taki amince wa da tayin da Liverpool ta mata na kusan £46M a farkon watan Augusta, wanda hakan yasa Liverpool ta sake tayin sa akan kudi £60M, amma dan wasan ya ki amince wa saboda sha’awan sa na buga kwallo a Chelsea.
Romeo lavia shi ne dan wasa na biyu daya zabi Chelsea maimakon Liverpool a satin daya gabata bayan Moises Caicedo wanda Chelsea ta sayeshi daga Brighton.

“Romeo Lavia” matashi ne dan shekara 19 wanda ya koma Southampton a shekara ta 2022 bayan buga zango biyu a Man City a shekara ta 2021.