Captain Bruno Fernandez Ya Sato Point 3 Wa Man United A Wasan Su Da Nottingham Forest
Nottingham sunsha Man United kwallo biyu wadda Taiwo Awoniyi da Willy Boly suka sha a Old Trafford, amma Man United sun rama kwallo biyu, sannan suka kara na uku bayan dan wasan Nottingham ya samu jan kati.
Awoniyi ya saka kwallo a ragar Man United a minti biyu na wasa, wadda yayi gaba-da-gaba da gola, sannan yaci kwallon a kasa a gefen dama.
A minti na 4 Nottingham suka sake jefa kwallo a ragar Man United, wadda aka ya yanko free kick, Willy Boly ya same ta da kayi har cikin raga ta gafen hanun dama.
Christian Eriksen ya rama kwallo na farko wa Man United a minti 17, Rashford ne ya bugo kwallon a kasa, Eriksen ya karasa ta da kafa zuwa cikin ragar Nottingham.
Casemiro ya sake cin kwallo wadda yasa suka dawo 2-2 da Nottingham a minti 52 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, wadda Rashford ya bugo a sama zuwa gaban ragar Nottingham, Bruno ya bawa Casemiro assist da kayi, shikuma ya buga kwallon zuwa cikin raga da kafa.
Joe Worrall ya samu jan kati a minti 67, saboda ya kama Bruno harya kaishi kasa a gaban raga a waje lokacin da yake kokari kai hari zuwa gidan Nottingham.
Man United sun samu “bugun kai tsaye da gola” (penalty) wadda defender ya saka kafa wa Rashford ya kwashe shi har kasa, Bruno Fernandez ne ya buga penalty ta hanun hagu gola yayi kokarin tarewa amma ta shiga.
Man United sun kwashe maki aku, Nottingham kuma sun koma gida babu maki ko daya.