Labaran Yau

Zaka Iya Rayuwa Cikin Gawurtaccen Gida Amma Ka Kasance Cikin Kunci – Adam A Zango

Shahararren Jarumin Kannywood da akafi sani da Adam A Zango ya danyi wata tsokaci kan maganganunda mutane keyi akan rabuwarsa da matayensa.

Jami’inmu na Labaranyau Blog ya kawo cikakken bayanin da Adam Zango yayi bayan ya saki bidiyo kan cewar zai rabu da matarsa.

Ga bayanin kai tsaye yanda ya rubuto a shafinsa na muhawar Facebook ⇓

Idan Gaskiya Ta Bayyana Mu Dage Mu Yadata Ga Al Umma Kada Mu Boye Don Kar Mu Baiwa Mai Wannan Gaskiyar Credit Dinshi, Saboda Bamu Sonshi

Masu hikima sunce zaka iya rayuwa a cikin gawurtaccen gida wanda ba’a rasa komai a cikin gidan ba. Amma ka kasance a cikin kunci da damuwa.

Wani kuma yana a cikin kauye a kauyenma a cikin bukka amma yafi mai wadata jin dadi da farin ciki da rayuwa mai dadi.

Jin dadin aure a zuciya take ba’a kyakyawan gida, kyawawan tufafi, tarin dukiya, kayan alatu ko kyan mace ko kyawun na miji ba. Soyayya babu dalili itace soyayya, ba soyayya mai dalili ba.godiya ga Allah ba ba yin sallah ko azumi ko zuwa ummara ne ba.

Kyautatawa iyali da arzikin da Allah S.W.T ya baka da kyautatawa Al’umma shine godiya ga Allah.

Mu zama masu yabawa juna idan akayi abin yabawa ko fadawa juna kuskurensu idan akayi kuskure.

MU AJIYE SON ZUCIYA, HASSADA, BAKIN CIKI, KYASHI, TSANA BABU DALILI, ITACE KADAI KOFAR BULLEWA A WURIN MUSULMIN AREWACIN NIGERIA

DOWNLOAD ZIP/MP3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button