Labaran Yau

Bazoum Ya Rubutowa ECOWAS Wasika A Sirrance

Bazoum ya rubuta ECOWAS, Amurka da EU ya ce ” sojojin da sukayi juyin mulki sunyi garkuwa da ni” Daga Mohamed Bazoum, Shugaban Jamhuriyar Nijar

Ina rubuta wannan wasika ne a boye. Kasar Nijar dai na fuskantar hare-hare daga gwamnatin mulkin soji da ke kokarin hambarar da dimokaradiyyar mu, kuma ina daya daga cikin daruruwan ‘yan kasar da aka daure ba bisa ka’ida ba.

Wannan juyin mulkin da wani bangare na sojoji suka kaddamar wa gwamnatina a ranar 26 ga watan Yuli, ba shi da wata hujja. Idan har ta yi nasara, za ta haifar da mummunan sakamako ga kasarmu da yankinmu da ma duniya baki daya.

Gwamnatinmu ta hau karagar mulki sakamakon zabukan dimokuradiyya a 2021. Duk wani yunkuri na hambarar da halaltacciyar gwamnati dole ne a yi yaki da shi, kuma muna jin dadin yin Allah wadai da wannan yunkuri na rashin gaskiya na kawo cikas ga ci gaban dimokuradiyyar Nijar.
Amurka da Tarayyar Afirka da Tarayyar Turai da kuma kungiyar ECOWAS sun yi kakkausar suka cewa: Dole ne a dakatar da wannan juyin mulki, sannan kuma dole ne gwamnatin mulkin soja ta sako duk wadanda suka kama ba bisa ka’ida ba.
Masu yunkurin juyin mulkin sun yi kuskuren cewa sun yi hakan ne domin kare tsaron Nijar. Suna da’awar cewa yakin da muke yi da ‘yan ta’adda masu jihadi ya ci tura, kuma mulkina na tattalin arziki da zamantakewa, gami da kawance da Amurka da Turai, ya cutar da kasarmu.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button