Labaran Yau

Kotu Tayi Watsi Da Karar Zakzaky Akan Takardan…

Kotu tayi watsi da karar Zakzaky akan takardar fita kasar Waje

Kotun tarayya dake Abuja ran Alhamis da ta gabata ta kori karar da shugaban Shi’a sheikh Ibraheem El-Zakzaky da Matarsa Zeena, wanda suke neman hukumar fita (Immigration) da su basu takarda fita kasar waje (Passport)

Alkali Obiara Egwuatu, a hukuncin shi masu kara basu bayarda hujjar su yadda takardar fitansu ta salwanta ba. Sunki su bayyana abinda ya faru da takardar akan koh konewa tayi, bata tayi koh da kwacewa akayi koh hukumar ne ta hanasu.

Shi El-Zakzaky da uwar gidansa su biyo ta hanun Babban lauyan kasa, Femi Falana, wanda ya danna karan kwantrola janar a meh neman kariya na daya da na biyu, a watan junairu a shekarar da ta gabata, 2022 akan hana takardar fita kasa wanda suka nema.

DOWNLOAD MP3

A cikin wanda aka danna musu kara harda kuman tsaro na NIA da SSS. A matsayin masu neman kariya na uku da hudu.

A takardar karan da suka kai meh lamba FHC/ABJ/CS/22/2022, suna neman a kwato musu yancin su wanda dokar kasa ta basu da shatan afrika na yancin dan Adam.

Sun bayyana cewa takardar su ta fita an karbe kuma an hallakar a shekarar 2015, bayan sojoji sun shiga gidansu.
Suna rokon kotu ta bayyana hana su cigaba neman takardar fitan su neman lafiya baya ka’ida kuma ya fita ka’idar doka.

DOWNLOAD ZIP

Lauyan (Immigration) hukumar kula da Shiga da fita Jimoh Adamu ya karyata cewa ba a hanasu ba kuma yasaka Ana kan bincike.

Shi lauyan A watan fabrailu ta 2022, ya fuskanci kotu akan hada Karan da akayi NIA da DSS.

Alkali Egwuatu ya hada masu kara El-Zakzaky da matansa a masu neman kariya na uku da hudu.

A yayinda ake yanke hukunci Alkalin ya bayyana ba masu neman kariya ake zargin ya karbi takardar ba, sai dai sun bayyana cewa an hallaka koh ya bata a lokacin da jami’an tsaro suka kai musu farmaki.

Yace “wannan kara munyi watsi da ita” inji Alkali Egwuatu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button