Labaran Yau

Yan Fanshon Najeriya Suna Neman Gwamnatin Tinubu Ta Yarje Musu Sabon…

Yan fanshon Najeriya Suna neman gwamnatin Tinubu ta yarje musu sabon ministry

hadakayyan yan fanshon Najeriya sun kira shugaban kasa meh jiran gado Bola Ahmed Tinubu ya kawo musu sabuwar ministry wanda zata kula da harkokin fansho da gyara wa masu ritaya a kasar.

Su hadakayyan yan fansho na kudu maso yamma sunyi kiran ne bayan tattaunawarsu wanda suka saba yi mako mako ran Alhamis a Abeokuta.

Tattaunawarsu ya hada jiga jigen kamar ciyamominsu, sakatarorin su na jahar Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Legas da Ekiti.

A maganan da sukayi da manema labarai bayan tattaunawarsu, meh sanarwa na hadakayyan Olusegun Abatan yace kirkiran ministrin fansho zai canza wa yan fansho rayuwa ya kawo musu jin Dadi a fadin kasar.

Suna meh kiran Bola Tinubu yayi wani abu akan yan fansho in ya karbi karagan mulki.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kokari akan yan fansho. Kuma ya taimaka musu Kuma Suna kiran Tinubu ya kara sa ido akan al’amuran yan fansho.

Yace suna son ministrin yan fansho wanda zai kawo sauyi da gyara wa yan fansho a gwamnatin Tinubu.

Mista Abatan yana zargin gwamnoni kudu maso yamma da rike kudin fansho da giratuti masu yawa.

Yana kiran gwamnoni da su tabbatar da karin kaso 30 cikin 100 na kudin fansho da wuri.

Ya kara da bayyana cewa a jihar Ogun, Ekiti da Osun sun biya fansho da giratuti karshe tun 2012.

Yace yan fansho dayawa Suna bin bashi harda wanda suka mutu ba a bawa yaransu ba.

Suna rokon da gwamnoninsu su ajiye san zuciya akan yan fansho.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button