Labaran Yau

An Sace Sakataren Tsare-tsare Na Jam’iyyar APC A Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da sakataren kungiyar APC, Hon. Kawu Ibrahim Yakasai, daga gidansa dake kauyen Yakasai a jihar Kaduna.

An yi garkuwa da mutanen ne da misalin karfe 10:00 na daren ranar Juma’a lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye kauyen Yakasai da ke karamar hukumar Soba.

Sun kai hari musamman gidan Yakasai inda suka dauke shi da karfi, kamar yadda majiya ta bayyana.
Maharan sun kama Kawu Ibrahim Yakasai, wanda tsohon Shugaban karamar hukumar Soba ne, daga bisani kuma aka dauke shi zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Da yake tsokaci kan lamarin, wani mazaunin garin na Soba, Lawal Sani, ya yi addu’ar Allah ya kubutar da tsohon shugaban daga hannun wadanda suka sace shi.
Wani mamban kwamitin gudanarwa na jam’iyyar mai mulki da ya yi magana a boye ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya nuna damuwarsa kan lafiyar Hon. Yakasai.

Mohammed Lawal Shehu, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna Uba Sani, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce Gwamnan ya umarci jami’an tsaro da su bi bayan masu garkuwa da mutanen tare da tabbatar da dawowar Yakasai lafiya.

Ya nanata kudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Kaduna.
Ya kara da cewa, daya daga cikin matakan da aka dauka domin cimma hakan shi ne kudurin sa na daukar ‘yan banga 7000 aiki, wadanda za su taimaka wa kokarin hukumomin tsaro a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, har yanzu bai mayar da martani da sakonnin da aka aike musu kan batun ba har zuwa lokacin da ake cike rahoton.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button