Bikin dai ya zo ne kasa da mako guda bayan da Shugaba Tinubu ya fitar da jerin sunayen wadanda aka nada, wanda ya sake duba shi a ranar Lahadi, kuma ya masa chanje chanje har guda 6.
An gudanar da bikin rantsar da ministocin ne a dakin taro na fadar shugaban kasa, Abuja a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, 2023.
Makonni biyu bayan kammala tantance sunayen ministoci 48 da majalisar dattawa ta yi, shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar da 45 daga cikinsu da aka tabbatar a wani biki da aka gudanar a dakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja ranar Litinin.
Wannan dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan da Tinubu ya fitar da jerin sunayen wadanda ya nada.
Ga hotunan taron a kasa:
An gudanar da bikin rantsar da ministocin ne a dakin taro na fadar shugaban kasa, Abuja a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, 2023. (Hoto: Taiwo Adesina)