Labaran Yau

Zulum Ya Zabi Tsohon Minista Bukar Tijani A Matsayin Sakataren Gwamnatin Jiha

Zulum Ya Zabi Tsohon Minista Bukar Tijani A Matsayin Sakataren Gwamnatin Jiha

Gwamna Baba Gana Zulum na jihar Borno ya amince da zaben tsohon ministan jiha akan noma da cigaban karkara, Bukar Tijani a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar, SSG.

Gwamnan ya amince da zaben Farfesa Isa Marte. A matsayin shugaban Ma’aikatan Gwamna.

Zaben guda biyu sun fito ne daga mai magana da yawun gwamna, Isa Gusau, a Jawabin da yayi a Maiduguri ranan Laraba.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Isa Ya ce Zulum ya amince da zaben Tijani saboda experience din da yake dashi a matsayin sa na Minista daga shekarar 2011 a watan Yuli zuwa satumba na shekarar 2013. Da Kuma mataimakin sakatare janar na FAO.

Bukar Tijani
Bukar Tijani

Bayan wannan ofishi biyu, ya bayyana wasu matsayin da ya rike a kasar harda Kodineta na kasa Hukumar kasa na noma da tsaro na abinci, da Kuma gudanar wa da yayi na aikin babban bankin Duniya ta fadama Project.

Isa ya kara da cewa tsohon ministan ya ziyarce kasashe hamsin dan yin abubuwa daban wanda zai kawo taimako wajen cigaban noma da tsaro a Najeriya. afirka da duniya baki daya.

Tijani dan shekara 62 an haifeshi a Damasak, amma shi dan garin dikwa karamar hukuma na jihar.

Yayi Firamare dinsa a Gubio daga 1970 zuwa 1973, yayi Makarantar firame na munguno shekarar 1967 zuwa 1970, Kuma ya yi sakandare na Yerba a Maiduguri daga 1973 zuwa 1978.

Bayan murna da akayi ma sabon sakataren gwamnatin jiha, gwamnan ya ba shi karfin gwiwa da cewa yayi amfani da experience din da yake dashi wajen aiwatar da aiki wa gwamnati mai inganci.

Ya nemi yasa hankali wajen kawo cigaba a hanyan noma da Kuma tsaron abinci, wanda shine abinda yafi ilimi akai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button