Labaran Yau

Shugaban Tinubu Ya Mika Ta’aziyarsa Wa Dahiru Mangal Da Imam Adigun

Shugaban Tinubu Ya Mika Ta’aziyarsa Wa Dahiru Mangal Da Imam Adigun

Shugaban kasa Bola Tinubu ya tura ta’aziyar sa shugaban Kampanin Jiragen Sama na Max Air da Da AFDIN,  Alhaji Dahiru Barau Mangal bayan rasuwar matarsa Hajiya Aisha, wanda ta rasu cikin karshen satin da ta gabata.

Shugaban kasan ya kara mika gaisuwar Ta’aziyya wa shugaban limamai na birnin tarayya, babban limamin Fouad Lababidi Central Mosque, da ke Wuse Zone 3 Abuja, Dakta Tajideen Adigun bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Aishatu Muhammad Adigun.

Hajiya Aishatu ta rasu ranan laraba Kuma an binne ta washe gari a garin Offa na jihar kwara.

Sakon ta’aziyar da Tinubu ya turawa mangal, yace yayi matukar jimami bayan labarin rasuwar matarsa ya iso masa.

A salon da ta Tinubu ya turawa Imam Adigun, Shugaban kasa ya ce wa Imam ya rungumi hakuri da kyakkyawan sunan da mahaifiyarsa ta bari na aiki kamin rasuwar ta.

Shugaban kasan ya bayyana sakon ta hannun mai magana da yawun sa, Dele Alake ranan litinin ya Kuma yi adduan Allah sanya ta a Aljannatul Fitdausi.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu buhari shima ya isar da nashi ta’aziyar wa Imam adigun.

Buhari ya tura sakon ta’aziyar sa wa Limamin wanda yake saudiyya domin aikin hajji ta bakin Mai magana da yawun sa, Shehu Garba.

Yayi adduan Allah ya jikanta da rahma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button