Labaran Yau

Dangote Yayi Tsare Tsaren Wadatar Da Najeriya Da Siminti Da Kuma…

Dangote yayi tsare tsaren wadatar da Najeriya da Siminti da man fetur

Kampanin dangote tayi tsare-tsare dan wadatar da Najeriya da siminti, Man fetur, kayan Noma da na duwatsun haka.
Darektan siya da siyarwa na yankin gudu maso gabas na dangote siminti, dakta Abayomi Shittu ya bayanar da haka a jihar Enugu ran Alhamis wanda akayi murnan ranar dangote a cinikayyar kasuwanci na 34 a Enugu.

Ita kampanin dangote, tayi nisa ne wajen samarda sugar, gishiri, siminti, gine gine da sauransu cikin kasuwanci da sukeyi. Suna da kampani guda uku wanda ta kunshi ta sugar, gishiri da siminti wanda suke karkashin NASCON wanda take Nigeria stock exchange.

Yace sun dage wajen fidda sabbin abubuwa domin inganta kampanin dakuma saka hannun jari a wanda zata bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ya bayyana cewa kampanin suga ta samar ma yan karkara aikin yi a kauyukansu ta inda suke noman rake kampanin nasu siya hakan ya hanasu zaman banza.

Zuwan dangote fertilizer ya kawo babban taimako Bun kasa noma da harkan gona, Kuma kampanin tace mai na dangote inta fara aiki zata kawo cigaba wanda babu misali a kasar.

Daraktan ya ce sun bada aiki wa wa inda suka gama jami’a da kwarewa wajen fasaha Kuma suka basu horaswa ta fanin gudanarwa.

Kampanin dangote tazo ne dan ta kawo canjin da yelwantuwar arziki da aikin yi wa mutanen najeriya.

Kampanin Tana da wasu shiyoyin kampanin su a kasashen afrika da yawa wanda ta diba mutane a fadin duniya dan mata ayi. Yace kiyascin 85 cikin Kaso dari na ma aikata yan Najeriya ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button