Labaran YauNEWS

Yajin Aikin ASUU – Buhari Yabawa Dalibai Hakuri

Yajin Aikin ASUU – Buhari Yabawa Dalibai Hakuri

Kazalika Buhari ya yi kira ga kungiyar ta ASUU da ta duba halin da daliban suke ciki, ta janye yajin aikin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi kira ga daliban jami’o’in kasar da su kara hakuri, yana mai cewa gwamnati na iya bakin kokarinta don ganin an kawo karshen yajin aikin da malamai ke yi.

Tun a watan Fabrairu kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ta ASUU ta shiga yajin aiki, a kuma farkon makon nan ta kara tsawaita shi har zuwa watan Agustan bana.

Kungiyar na zargin gwamnati da abin da ta kira “rashin kulawa” da gwamnati ke nunawa wajen neman maslaha kan batun.

Sai dai yayin taron karrama masu hazaka na kasa da aka yi a Abuja a ranar Alhamis, inda aka ba mutanen da suka yi fice lambobin yabo na NPOM a karo na 19, Buhari ya yi kira ga daliban da su kara hakuri kan halin da suke ciki.

Gwamnati na iya bakin kokarinta wajen ganin ta lalubo bakin zaren wannan matsala da ta ki-ci-ta-ki-cinyewa a jami’o’in kasar tare da yin la’akkari da iya karfin da muke da shi.” Wata sanarwa da Kakakin Buhari Femi Adesina ya rabawa manema labarai ta ce.

Kazalika Buhari ya yi kira ga kungiyar ta ASUU da ta duba halin da daliban suke ciki, ta janye yajin aikin.

Buhari ya kuma tunatar da cewa, “ya ba shugaban ma’aikatan fadarsa, da ministocin kwadago da na ilimi da kudade, da na tsare kasafin kudi umarni, da su yi maza su gayyato dukkan masu ruwa da tsaki kan teburin sulhu don a duba bukatun na ASUU.”

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button