Labaran Yau

Jamb Zata Sanya Yaran Da Ke Karatu A Sudan A Wasu Jami’o’i

Jamb zata sanya yaran da ke karatu a Sudan a wasu jami’o’i

Hukumar jarabawa ta kasa Jamb, tayi alkawarin saka yan Najeriya da aka dawo dasu daga kasar sudan saboda yakin da kasan ke ciki, zuwa wasu makarantun jami’a dake kasan Najeriya.

Rajistaran Jamb, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana hakan a Abuja bayan shugabar Hukumar mutan Najeriya an waje Abike Dabiri ta kai mai ziyara.

Ziyarar anyi ne dan hada kan daliban zuwa wasu jami’o’i, saboda yanayin da suka tsinci kansu ciki na katsewar karatu.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Oloyede, wanda ya tausaya wa daliban da kuma yaba Hukumar mutan waje, wajen aiki da sukayi tukuru dan fidda yan kasa Najeriya daga cikin tashin hankali na yaki duka tsinci kansu ciki. Yayi Alkawarin jamb zata basu taimaka.

Rajistaran Jamb din ya bayyana cewa wanda suka dawo daga Ukraine, sunki bin ka’idoji dan cigaba da karatun su a Najeriya.

“Zamuyi kokari wajen bada wuri Mai kyau da Kuma duk abubuwa da ake bukata wajen dawo dasu karatu. A cewar sa

“Dole mu godewa NIDCOM wajen hazaka dan taga daliban sun dawo karatu a makarantun Najeriya, Kuma mun basu hanyoyi da zasu bi dan samun cigaban hakan.

“Akwai hanyoyi na canjin makarantun kamar takardan sakamakon jarabawa na makarantun da sukayi a sudan da sauransu.

“Kar kowa yayi tunanin zai samu satifiket in beyi shakara biyu a jami’ar Najeriya ba.

“Hanyoyin da za a bi Suna cikin dokokin Hukumar jami’an kasa da Kuma makarantun da suka fito.

“Dokokin da aka gindaya yana hannun ita shugabar Madam Dabiri” cewar Oloyede.

Ya ce dalibai subi dokokin canjin makarantun da. Samun cigaba karatu, Kuma in kana aji shida ne, za a yi gwaji in daliban sunci za a basu aji biyar Sai su karasa karatun su.

Kuma Duk dokokin da aka sanya Tana website din jamb na yanar gizo.

Dabiri ta bayyana cewa mafi yawan wanda suka dawo dasu daga sudan dalibai ne wanda suke son su cigaba da karatun su. Tace duka dokokin za a bisu.

Wata magaifiyar dalibi Asmau Yerima, ta yabawa Hukumar NIDCOM da Jamb wajen wannan cigaban da Kuma kawo sauki wa daliban dan samun cigaba da karatun su.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button