Duk Yen Takarar Shugabancin Nijeriya Bawanda Yakai Bala Muhammad – Kungiyar Niger Delta
ZABEN 2023: Daga APC Har Zuwa PDP Babu Dan Takarar Shugaban Kasa Da Ya Kai Bala Mohammed Cancanta, Cewar Kungiyar Niger Delta
Wata kungiya daga yankin Niger Delta (NDRO) ta bayyana Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed a matsayin mafi cancanta cikin ‘yan takarar da suke neman kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyun APC da PDP.
Kungiyar ta kara da cewa abin burgewa ne yadda ‘yan Nijeriya suka fuskanci gaskiya suka marawa dan takara mafi cancanta baya, wanda zai iya ceto kasar daga fadawa mawuyacin halin da za ta iya shiga idan har ta fada hannun zabin da ba nagari ba daga cikin jam’iyyun APC da PDP.
Kungiyar ta bakin kakakinta, Odoginyon Adetunbosun, ta bayyana Sanata Bala Mohammed a matsayin dan kasa nagari, wanda ba zai nuna bambanci ba a matsayin sa na shugaba. Inda ta kawo hujja da cewa kasancewarsa Gwamna Bala wanda ya rike mukaman Sanata, Minista kuma yanzu yake kan kujerar Gwamna, yana da makamar sanin aiki wanda sauran ‘yan takarar ba su da ita.