Hotuna: Shetima Yakai Gaisuwar Ta’aziyya Wa Iyalen Dan Uwansa
Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shetima yau yakai gaisuwan Ta’aziyya gidan iyalen dan uwansa, Mukhtar Alkali a Maiduguri, Jihar Borno.
Mataimakin shugaban kasan wanda yaje gidan marigayi Alkali da Gwamnan Borno Babagana Zulum, da wasu jiga jigan gwamnati Duk sun je gidan tsohon Ma’aikacin gwamnatin.
Shi mataimakin shugaban kasa da Gwamna Zulum sun hadu sunyi addua wa marigayi Alkali da iyalensa.
Marigayi ya kasance tsohon Provost kwalajin noma na Jihar Borno, Maiduguri.
Ya jima yana yunkuri wurin samar da aiki wa samari dan shine mafita kan kalubalen talauci da rashin tsaro a kasar.
Ta’aziyar ya hada manyan mutane na kasar, malaman Addini, sarakunan gargajiya, harda Shehun Bama, Umar Shehu Kyari.
Marigayi Alkali ya rasu ranan jumma’a yana da shekara 57, Kuma an binne shi daidai da koyarwa ta addini.
Olusola Abiola, Daraktan Zantarwa na mataimakin shugaban kasa ya bayyana hakan.