Labaran Yau

Banyi Nadaman Auren Yar Shekara 15 ba – Yerima

Banyi Nadaman Auren Yar Shekara 15 ba Cewar Sanata Ahmed Sani Yerima

Banyi Nadaman Auren Yar Shekara 15 ba – Yerima

Tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yerima yace bai yi na daman auren yarinya yar shekara 15 wanda suka hadu a Egypt.

Sani Ahmed Yerima ya bayyana hakan yayin tattaunawan sa da yayi da channels Tv a shirinsu na siyasa a yau.

Yerima ya karyata cewa matarshi ba yar shekara 13 ne ya aureta ba.

“Mutane basu san cewa akwai abubuwa da ake yi wanda ba kan doka ba ne, wanda ke a wajen doka, da zai sa kayi nadama.  Dokar shari’a, yanada daga cikin dokar kasar Najeriya ta yarda da hakan, idan yarinya ta kai munzali to takai na aure.

“Bawai Sai yarinya ta kai shekara 18 ko 20 ba, babu wani abu akan shekaru, yadda akeso mace ta kai na aure yana cikin tsari na dokar shari’a.

“Dayawa daga cikin yarana mata sunyi aure a wannan shekarun, Suna tare da iyalensu Kuma babu damuwa, dukan su sunyi karatun degree a jami’a, daya daga cikinsu wanda na aurar a shekara 16 Yanzu haka Tana PHd dinta a london.

Shekaru Goma da suka wuce yan jarida sunyi ta babatu kan batun sa na auren yarinya Yar shekara 13 wasu suce 14. Wanda mutane daya suna tunanin hakan ba daidai bane Kuma ta ke yancin yara matane.

Dan mutane dayawa daga kudancin Najeriya sukan fadi hakan ko cikin wasa ko tsokana cewa auren yara a arewancin Najeriya baida kyau wanda ake kwatance da Sanata Yerima da yin hakan cewar bai dace ba.

Shari’ar Muslunci ta zo da dokoki, da ka’idoji na yadda ake bi wajen aurar da yara mata, wanda hakan bai hana Yerima auren matarsa Yar shekara sha biyar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button