Labaran Yau

Yan Sanda Sun Bayyana Dalilin Yawan Jami’an Tsaro A…

Yan sanda sun bayyana dalilin yawan jami’an tsaro a jigawa

Yan sanda sun bayyana dalilan da yasa aka saka jami’an tsaro da yawa a jihar jigawa dan magance matsalolin da zasu iya aukuwa a zaben da akayi ran asabar.

Kwamishinan yan sandan Effiom Ekot ya bayyana cewa, yawan yan sandan yazo ne bisa zaben ba dan karamin bam da ya tashi bane cikin kwanakin wanda ya ma mutum daya rauni ba.

Ekot ya bayyana hakan ne a wajen ganawarsa da manema labarai akan zaben da za a sake na yan majalisun jiha a kananan hukumomi biyar ta jihar.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Hukumar labarai ta kasa ta bayyana cewa na’ura ce ta tashi a unguwar hakimi a garin dutse tayi wa dan kasuwa Friday fryo rauni.

Tun Wannan lokacin sojoji sun tashi tsaye wajen tsaro a ko wane checkpoint na jihar.

“Muna so mu nunawa mutane cewa Muna nan Kuma baramu bar wani abu da zai kawo tashin hankali ba. Kuma mutane su sani baramu lamunci wani abinda zai kawo tarzoma ba.

“Ina so mutane su samu nutsuwa, yawan jami’an tsaro wanda ya hada da soji da yan sanda dan samun zaman lafiya ne.

“Muna son hadin kan jama’a dan martaba jihar da tafi kowani jiha zaman lafiya a Najeriya” a cewar kwamishinan

Yace aiki sukeyi ba dan su tozarta kowa ba Kuma barasu tozarta kowa ba.
Ya shawarci shuwagabannin gargajiya da na addini dasu zama masu lura da mutane da Kuma fadakarwa dan a samu a magance Duk wani abinda zai kawo tashin hankali a jihar.

Duk wanda sukeyin kasuwanci Mai tsafta kar suji tsoro, jami’an zasu zama musu kariya ne inji shugaban yan sandan.

DailyNigeria ne suka rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button