Wasu ‘yan bindiga daɗi kai hari a Custom Base da ke garin Koko a jihar Kebbi, inda suka yi sanadin mutuwar jami’in guda daya tare da yin garkuwa da wani.
Harin ya faru ne a ranar Alhamis, 25 ga Yuli, 2024, kusan karfe 9:00 na dare. Ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun yi mummunar barna a sansanin kafin su bi sawu tare da kai wa jami’an biyu hari.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, Mohammed Tajuddeen Salisu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yammacin Lahadi.
Bayanin Tajuddeen Na Harin Custom Base A Kebbi
PRO Kebbi Area Command, Muhammed Tajiddeen Yace:
“Cikin nadama, mun sanar da wani abin takaici da ya faru a sansanin mu na sintiri na Koko Besse a ranar Alhamis, 25 ga Yuli, 2024, da misalin karfe 2100.
“Wasu ‘yan bindiga sun kai hari sansanin ‘yan sintiri, inda suka lalata kadarori tare da kai wa jami’an mu hari a wata fafatawar da suka yi na inganta ayyukan fasakwauri a yankin,” in ji Salisu.
“An harbe jami’in daya sannan aka yi awon gaba da daya.
“Sai dai abin takaicin shi ne mataimakin Sufeton Kwastam na daya Dabo Umar ya rasa ransa yayin da aka yi garkuwa da Sufeto Babagana Abba Kabiru sannan aka bukaci a biya shi makudan kudin fansa domin a sake shi.” Inji Tajuddeen.