Labaran Yau

Dangote Ya Nemi Duniya Ta Kawo Karshen Cutar Malaria Kamin..

Dangote ya nemi duniya ta kawo karshen cutar Malaria kamin 2030

Shugaban kampanin Dangote, Aliko Dangote, ya nemi hadin kai a duniya don kawo cigaba na magance matsalar cutar cizon sauro gabadaya a shekarar 2030.

Dangote da ambasadan najeriya na Majalisan dinkin Duniya (United Nations), sunce maida hankali da saka hannuwa dan kawo rashin yaduwar cutar cizon saura shi yakamata a sa a gaba, A jawabin ranan cutar malaria ta duniya.

A fadin sa, ya bayyana cewa duka dakarun kasashe yakamata su Zauna suyi aiki tare dan kawo karshen cutar, dan cutar ta bada mummunan gudumawa daga rashin lafiya Sai koma baya ta fanin bunkasuwan kasuwanci.

DOWNLOAD MP3

Ya kara jaddada cewa sabbin hanyoyi da karfafa su shine mafi Alkhairi wa dakarun kasashe dan magance yaduwar cutar.

Dangote ya ce tun shekarar 2000, hadin gwiwa na duniya da saka hannuwa ya taimaka wajen rage yaduwar cutar malaria wanda matakan da aka bi ya hana mutum biliyan biyu kamuwa da cutar Kuma ya kawo waraka ga mutum miliyan sha daya.

Ya ce kashi 96 cikin dari na mutuwa da akeyi ta malaria yana samuwa ne a kasashe 29 wanda Najeriya Tana na hudu wanda yazo da kusan Rabin mutuwa daga cutar a shekarar 2021.

DOWNLOAD ZIP

Attajirin dan kasuwan ya bayyana a shekarar 2023 na ranan malaria ta duniya ta nuna zage damtse wajen magance cutar.

Dangote ya bayyana shirin sa na jagorancin wannan tafiya da gidauniyar sa, da yin aiki da jiga jigen don samun maslaha da cimma burin kawo karshen cutar a shekarar 2030.

“Ba kamar da ba, Zamu hada kai dan kawo karshen wa yara da manya dan kamuwa da cutar.

“Zamu yi iya kokarin mu dakile cutar ta malaria a kasar najeriya da Afrika gaba daya.

“Za a sa daci a wurare uku wanda sun hada da saka dakile cutar yazama muhimmi wa idon najeriya.

“Zamu cigaba da bayyana a kawo wani mataki dan samun isheshshen kudi dan aiwatar da kudirin mu na dakile cutar dan samun cigaba a yaki da cutar.

“Zamu bawa yan kasuwa shawara da karfin gwiwa dan daukan matakai wajen yaki da cutar kamar yadda akeyi kampanin Dangote.

“Idan Afrika zata cigaba, Toh Sai ta tsaya a tsaye dan daukan matakin da zata taimaka wajen kawo karshen malaria dan cigaban nahiyar zuwa shekarar 2030”. Ya ce

Daily Nigeria ta rawaito cewa ya yabi Najeriya wajen jajircewa da kuma Hukumar kula da lafiyan abinci da magani (NAFDAC) dan kokarin da sukeyi da Kuma amincewa amfani da magani R12.

Dangote yace a yayin da kasashe ke bukatar isowan magunguna, yakamata su kula da ta inda suke samun magani, ta inda zai kawo sauki kamar yadda akayi Na dakile polio.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button