AddiniLabaran Yau

Wasiyar Annabi SAW Ga Abu Hurairah RA

Annabi SAW ya kira Abu Huraira Yace Zan maka wasiyya da wasu ababe guda uku, Duk halin da kake ciki a rayuwa kada kayi sake a kansu.

Wadannan ababe guda uku karike su na hakika, bahaushe yana wata karin magana yace wanda bai da uba idan yaji uban wani na magana Sai ya saurara.

Bamu rayu da fiyayyen halitta ba, Sai ya kira wani sahabinsa wanda yake sonsa Sai ya bashi wani hanyar tsira. Kaga idan munada dabara Sai mu karbi wannan abun mu rike shi hanu bibbiyu.

Yana cewa Annabi ya bani wasu abubuwa Kuma yace min har na rasu kar na rabu dasu. Kar kayi wasa dasu har ka mutu.

Na farko karka bari a fara wata har a gama bakayi Azumi a kalla guda uku ba. Ko Litinin Litinin koh Alhamis Alhamis ko sha uku sha hudu sha biyar na kalandar Musulunci.

A Duk wata da zai shiga ya fita kar kayi sake kar azumi guda uku su wuce ka ko su gagareka, Annabi yace karka kuskura.

Mai ya dace mu muyi, ya dace mu mu dauka, in acikin mu akwai wanda baya azumi uku a wata inyanada da bara yana jin wannan Sai yayi kokari ya dauka. Shima daga nan kar ya kara sake.

Saboda shi azumin tarbiya ne, in baka saba ba haka zai rinka baka wuya kamar gudu ne. Wanda kullum zai ci abinci ya koshi kullum Ana tuka shi a mota in kace yayi gudu ai ka hada shi da aiki.

Amma in ya fara kadan kadan Sai kaga kamar bashi ba, Toh Azumi shi ma haka yake, amma in ka saba da yi kadan kadan in ance ka bari barin ma Sai yazama kamar punishment Ake maka.

Na biyu yace da salatul Duha, Sallar walha, Annabi yace a kowani hali kake yace kayi sallar walha. Duk wurin da ka samu kanka kayi sallar walha acikin sa.

Mafi kankanta Raka’a biyu, wasu malamai sunce Hudu, wasu sunce shida wasu sunce takwas. Amma dai za ka iyayi daga biyu zuwa takwas.

Na Uku yace Duk dare kar ka bari sallar wutr ya wuce ka, kayi kamin ka kwanta barci. Koh da a gajiye kake kasan in ka kwanta ba lallai ka iya tashi ba. Toh ba dole bane Sai kayi shafa’i, hanzarta kayi wutr Raka daya yayi. In shaa Allah tayi.

Amma in ka hada ta shafa’i, to wannan yafi dadi kamar ka girka abinci ne kasaka dan manda acikin sa. Annabi yace kar kuskura ka bari wannan ta kubuce maka Duk rana.
Allah yasa mu dace.

Ga bidiyon anan ⇓

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button