Labaran Yau

Malami Zai Fuskanci Majalisan Tarayya Kan Kudin Mai Dala Biliyan..

Malami zai fuskanci Majalisan tarayya kan kudin Mai dala biliyan biyu

Lauya janar na kasa, AGF Abubakar Malami, ya nuna shirin sa dan bayyana gaban kwanitin bincike wajen zargin da ake na kudi biliyan biyu da digo hudu wanda ya bata kuma ba a sa cikin asusun kasa ba, a majalisan tarayya.

An samu harajin kudaden ne wajen sayar da mai wanda akayi ba bisa ka’ida ba, har ganga miliyan 48, wanda aka fitar tun shekarar 2014 zuwa yanzu.

Malami yace zai bada duka bayanin akan zargin da akeyi na sayar da mai ganga miliyan Arba’in da takwas wanda yakai kudi dala biliyan 2.4 wanda aka fitar zuwa kasashen waje daga 2014 zuwa yau.

Mista Gbillah, bayan amsan takardar da ministan Adalci ya turo, ya bayyana cewa sun karbi takardar da Kuma bayyana ministan a mai bin doka.

Kuma kwamitin Suna mamakin saurin rubuta musu takardar wanda basuyi tsammanin abu haka cikin karamin lokaci ba, Kuma amsa gayyata akan zai halarci Majalisan tarayya ran Alhamis.

A halin da ake ciki ministan kudi har yanzu bata ce komai kuma babu koh labarin ta.

Suna so ita ministan kudi ta daraja mukaminsu na yin aikin da ya ajiye su a majalisa Kuma ta amshi gayyatan dan bin doka.

Wanda hakan zai taimaka wajen kammala aikinsu na bincike inji cewar Gbillah.

Hukumar labarai ta kasa ta bayyana cewa, bayan dawo da bincike da akayi, kwamitin tayi tambayoyi wa kampanonin mai da suke da hadakaiya wajen fitar da mai kasashen waje.

Daily Nigeria ta rawaito cewar duk dai akan kudaden ne da aka siyar da ganga miliyan 48 daga 2014 zuwa yau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button