Labaran Yau

Ministirin Tattalin Arzikin Dijital Zata Kashe Naira Biliyan 41.6 Dan Samar Da Na’urar Cudanya Da..

Ministirin tattalin arzikin Dijital zasu kashe Naira biliyan 41.6 dan Samar da na’urar cudanya da yanan Gizo- cewar Pantami

Ministirin sadarwa da tattalin arzikin dijital ta shirya dan Kashe kashe kudade daga asusunta na naira biliyan 41.6 dan samar da na’ura wanda keh hada mutane da yanan gizo a jami’un karatu, filin jirage da kasuwanni.

Hira da manema labarai ran Alhamis a Abuja, ministan, Farfesa Isa Pantami ya bayyana cewa kudin naira biliyan Arba’in daga Asusun Hukumar sadarwa ta Najeriya ne NCC.

A cewarsa kudin zai kawo sauki a makarantun Jami’a dari da goma sha uku 113, filin jirage da kasuwanni. “Kudin da Zamu kashe yakai Naira biliyan 41.6 a kiyasce.

DOWNLOAD HERE

“Jami’ar guda goma sha tara, kwalajin karatu guda daya, kasuwanni guda Ashirin, wanda zamuyi na biyu da na uku an shirya wa filin jirage Ashirin, karin kasuwanni guda shida, da jami’a guda Arba’in.

“ duka kudaden zamu kashe su ne don yin wannan aiki daga Asusun mu ne kuma baramu ci kwandala ciki ba”

Ayyukan da muka fara na farko yakai kashi 70 zuwa 90 a kaso 100, wanda za a fara na biyu da na uku wanda zasu shafi makarantu, filin jirage da kasuwanni.

DOWNLOAD MP3 HERE

Pantami ya kara cewa ya gamsar da shugaban kakakin NCC Farfesa Adeolu Akande da mataimakinsa Farfesa Umar Danbatta akan a kashe kudaden a fannin kasuwanci da ilimi.

“A halin da muke ciki kudaden da muke iya samu a sashin mu wasu sashin basu iya samu. Sai yasa yake da amfani mu saka kudin a wuraren da basu samu sosai”

Ministan ya bayyana cewa zasu cigaba da samar da abubuwa wanda ya shafi Al’umma a wasu sashin dan hidima wa mutane.

“Na samu rahoton ayyukan da aka gudanar a ayyukan mu na farko akan wannan projet ran 24 ga watan nowamba, 2022. Kuma a halin yanzu Zamu iya cewa aiki ya kammalu”

“A wannan lokacin Zamu fara gudanar da na biyu dana uku “ a cewar sa.

“Mun kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari dan sa hanu da amincewarsa, Kuma ya amince dan fara aikin na biyu dana uku aikin”

DailyNigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button