Labaran Yau

Dan Kasuwa Femi Otedola Ya Samu Ribar Naira Biliyan….

Dan Kasuwa Femi Otedola Ya Samu Ribar Naira Biliyan 71 Cikin Mako Guda

Arzikin dan kasuwan nan na Najeriya Femi Otedola dan asalin Jihar Lagos kuma Mahaifin shararriyar mawakiya Dj Cuppy, ya karu da sama da Naira biliyan 71 sakamakon kyakkyawan aiki da sabon kamfanin sa na Geregu Power yayi.

Kamfanin Geregu zai taimaka wa Otedola bisa sauye-sauyen da ya samu a matsayin da yake da shi da bankin First Bank of Nigeria a baya.

Geregu Power Plc, kamfanin samar da wutar lantarki da Otedola yake aiki a kai a halin yanzu, kamfanin ya kunshi wata babbar yarjejeniya da gwamnatin jihar Legas.

DOWNLOAD HERE

Femi Otedola ya samu Karin kudade cikin arzikin sa da ya zarce Naira biliyan 71.6 cikin kwanaki bakwai. Kyakkyawan aikin Geregu Power shine abin godiya a wannan karon , inda Otedola ke rike da matsayin babban mai hannun jari da jimlar 2.38bn (2,388,922,308).

Bincike ya nuna cewa tsakanin 6 ga Yuli, 2021 zuwa 14 ga Yuli, 2023, farashin hannun jarin Geregu Power ya tashi da kashi 10% wanda hakan ya taimaka wajen kara adadin hannayen jarin Otedola daga Naira biliyan 716.67 zuwa Naira biliyan 788.34.

DOWNLOAD MP3 HERE

Geregu Power ya kasance cikin labarai kwanan nan bayan kaddamar da wani gagarumin shiri na bunkasa aikin watsa wutar lantarki da kamfanin yayi.

Za a yi aikin ne tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Legas a ƙarƙashin tsarin haɗin gwiwar jama’a da masu zaman kansu (PPP). Otedola ya sanar da hakan ne bayan ya gana da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da Dr Akinwunmi Adesina, shugaban rukunin bankin ci gaban Afirka.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Otedola yayi kyakkyawan fata kan tattaunawar da ke gudana, wanda ke nufin kafa aikin watsa wutar lantarki na PPP na farko a Najeriya.

Sanarwar ta ce: “Tattaunawar wutar lantarki tare da Shugaban Bankin Raya Afirka, Akinwumi Adesina, da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.” Mun tattauna game da bunkasa aikin watsa wutar lantarki na gwamnati da masu zaman kansu na jihar Legas, wanda shi ne na farko a Najeriya.

Ana sa ran Geregu Power Plc zai taka rawar gani a fannin watsa wutar lantarki a fadin Jihar ta Lagos.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button