Kwamishinan ‘yan sandan jihar Lagos, Mr. Adegoke Fayoade, ya shawarci mazauna jihar da karsuyi niyyar kai wa masu zanga-zanga hari.
Kwamishinan ‘yan sandan ya yi gargadin cewa harin masu zanga-zangar na nufin daukar doka ne a hannun mutum.
Fayoade ya bayar da wannan shawarar ne a lokacin da yake jawabi ga sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma a kananan hukumomin Eti-Osa, Ibeju-Lekki, Epe da Lagos Island yayin wani taro da aka yi a ranar Asabar.
Ya ce ko da yake ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun gana sun bayyana cewa bai kamata a yi wata zanga-zanga a jihar Lagos ba, amma bai kamata mazauna yankin su farmaki wata kungiya da za su fito zanga-zangar ba.
Shirin CP Na Bada Kariya Da Kiyaye Lafiyan ‘Yan Kasa A Jihar Lagos
CP yayi kira ga jagororin zanga-zangar da su nuna kansu dan tafiyar da aikin ‘yan sanda me tasiri a ranar 1 ga watan Agusta dake zuwa.
Yayin da yake kira da shuwagabannin da zasu jagoranci zanga-zangar in har sai ta faru, yace lallai hakan na da amfani domin sanin irin tsarin da ‘yan sanda zata bi domin tabbatar da lumana a zanga-zangar.
Yace sanin wannan bayani zai taimaka sosai wurin samar da kariya da kuma kare lafiyar ‘yan kasa a ranar zanga-zangar domin cin ma burin ‘yan kasa.
Jawabin CP Adegoke Fayode Akan Zanga Zangar Jihar Lagos
“Idan dole ne a yi zanga-zanga, dole ne a yi a zaman lafiya. Muna so mu san masu son yin zanga-zangar domin mu yi tanadin tsaro.
“Hakkinku ne ku yi zanga-zangar bisa gaskiya matukar bai shafi hakkin wasu ba.
“Duk wata kungiya da ke shirin gudanar da zanga-zanga ta sake tunani. Irin wannan kungiya za ta gana da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro. Ba ma son maimaita #EndSARS.
“Aikin mazauna shi ne su baiwa ‘yan sanda bayanai kan lokaci game da duk wata kungiya da ke shirin gudanar da zanga-zanga, ba wai su kai musu hari ba,” in ji shi.