Labaran YauNEWS

Gwamnatin Kano Zata Kashe 3.5 Biliyan Na Daukar Nauyin Karatun ‘Yan Kano A Kasashen Waje

Gwamnatin Kano Zata Kashe 3.5 Biliyan Na Daukar Nauyin Karatun ‘Yan Kano A Kasashen Waje

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta kashe kimanin Naira biliyan 3.5 wajen bayar da tallafin karatu ga dalibai 550 domin yin karatun digiri na biyu a kasashen waje.

Dr Yusuf Kofar-Mata, Kwamishinan ilimi mai zurfi, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Kano, lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa na jihar na mako-mako.
Mista Kofar-Mata ya ce daliban za su yi karatu a jami’o’i bakwai a Indiya da Uganda.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Mista Kofar-Mata ya ce daliban za su yi karatu a jami’o’i bakwai a Indiya da Uganda.

Kwamishinan ya ce an zabo wadanda suka amfana 550 daga cikin dalibai 1,250 da suka nemi tallafin.

Mista Kofar-Mata ya ce gwamnati ta kusa kammala sarrafa biza ga daliban, wadanda za su fara tafiya a karshen watannan da muke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button